Tuesday, November 11
Shadow

An Hango ‘yan bìndìgà 300 a kan babura dauke da muggan makamai suna tafiya daga Zamfara zuwa jihar Naija

Akalla mutane 300 da ake zargin ‘yan bindiga ne, dauke da muggan makamai Akan babura, an hango su suna ketare hanyar Kontagora zuwa Minna, tsakanin Kampanin Bobby da Wamba a Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da rana tsaka, inda hakan ya sa direbobi da fasinjoji suka tsere domin kare rayukansu.

Wani ganau ya bayyana cewa, an yi imanin cewa ‘yan bindigar sun fito ne daga Jihar Zamfara, kuma suna tafiya cikin ‘yanci zuwa Karamar Hukumar Mashegu ba tare da gamuwa da jami’an tsaro ba.

Wani direba da ya shaida lamarin ya ce babu ko da jami’in tsaro guda daya a lokacin da lamarin ke faruwa.

Karanta Wannan  Tunda kamawa ake, Nima Nace Tinubu bashi da lafiya>>Matashi yace yana son a kamashi

Shugaban Karamar Hukumar Mariga, Abbas Kasuwa Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntube shi. Ya bayyana cewa an tura hadin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin domin kare al’umma.

Haka kuma ya bayyana cewa, wasu ‘yan sa kai guda biyu daga Wamba sun rasa rayukansu bayan fafatawa da ‘yan bindigar, yayin da wani guda kuma ke karbar magani a asibiti.

Rahotanni sun kara nuna cewa dakarun soji da ke sansanin Beri sun fara motsawa domin tunkarar miyagun.

An yi ƙoƙarin tuntubar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, bai yi nasara ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Tun ina Yarinya 'yar Shekara 5 na gano karyar da ake mana a coci, daga nan na ji soyayyar Annabi Muhammad(Sallalahu Alaihi Wasallam) ta shiga Raina kuma na zabeshi a matsayin Masoyi, Munirat Abdulsalam ta gayawa Kiristoci masu ce mata ta koma Kirista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *