Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sallami gaba ɗaya kwamishinonin jihar, inda ya ce ya na so ne ya kawo sabon-jini.
A jawabin a yayin taron sallama da kwamishinonin a gidan gwamnati, Eno ya ce dukkan su babu wanda bai yi kokari a muƙamin da aka bashi ba.
Sai dai ya ce duk da ko wanne daga cikin kwamishinonin ya yi kokari a ma’aikatar sa, akwai buƙatar a kawo wasu sabbin kwararru domin ci gaban jihar.