
Wata mata a jihar Bauchi me suna Salamatu Danjuma me kimanin shekaru 25 ta kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka.
Lamarin ya farune a garin Nadago dake karamar hukumar Tafawa Balewa.
Kakakin ‘yansandan jihar, Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin inda yace rikici kan rikon diyarsu ne ya jawo fadan da ya kai ga matar ta dabawa mijinta wuka.
An kai mijin Asibiti inda likitoci suka tabbatar da ya mutu.
Kwamishinan ‘yansandan jihar,Auwal Mohammed ya bayar da umarnin yin bincike sosai akan lamarin.