Wednesday, April 29
Shadow

Mu na fama da matsanancin ƙarancin ma’aikata – NAFDAC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC, ta koka kan matsanancin ƙarancin ma’aikata.

Da ta ke ganawa da manema labarai a Legas a jiya Alhamis, shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ta baiyana cewa a yanzu haka hukumar na da ma’aikata dubu 2 kacal a fadin ƙasar, inda ta ce hakan adadi ne mai matuƙar kankanta duba da irin aikin hukumar.

Ta yi kira da a ninka adadin ma’aikatan hukumar sau biyu ko sau uku, inda ta ce aikin da su ke yi na kare lafiyar al’ummar ƙasa baki daya na buƙatar wadatuwar ma’aikata don a samu sakamako mai kyau.

Karanta Wannan  Tanko Yakasai yayi kiran Arewa ta ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu saboda kokarinsa na tada komadar tattalin arziki na samar da sakamako me kyau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *