
Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya bayyana cewa, babu wata matsala a cikin iyalinsa, bayan da diyarsa ta zargi cewa yana yunkurin kashe ta da diyarta dan yin tsafi dasu.
Diyar Gwamnan me suna Jane, ta zargi cewa, haka mahaifiyarta da ‘yan uwanta biyu suka mutu inda ake zargin baban nasu da kashesu ta hanyar tsafi.
Saidai a martaninsa, Gwamnan yace ana kokarin kawar masa da hankali ne a aikin da yake yi a matsayinsa na Gwamna.
Yace wannan tsohon bidiyone kuma a yanzu da yake kokarin bayyana irin ayyukan da gwamnatin sa ta yi a cikin shekaru 2 da yayo yana Gwamna, shine aka dauko tsohon bidiyon ana yadawa.