Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya sanar da diyarsa Helen a matsayin wadda zata zama first Lady a jihar bayan mutuwar matarsa, Pastor Patience Eno.
Ya bayyana hakane a yayin da tawagar matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta kai masa ziyarar ta’aziyyar rashin da yayi.
Ya bayyana cewa, yana da yakinin diyar tasa zata iya rike wannan mukami yanda ya kamata.
Yace zata yi aiki tare da mataimakinsa da kuma kwamishiniyar harkokin mata ta jihar.