Thursday, January 16
Shadow

Gwamnan Zamfara ya ɗauki nauyin karatun zaƙaƙuran ɗaliban jihar

Gwamnan jihar Zamfara a arewacin Najeriya ya ba wa wasu zaƙaƙuran dalibai 30 tallafin karatu domin su yi karatu a sakandiren gwamnatin tarayya ta Federal Government Academy da ke Suleja ta jihar Neja.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da yake ganawa da ɗaliban da kuma jagorancin Cibiyar Muhammad Kabir Danbaba Centre for Women and Youth Development Center a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce cibiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da jihar ta Zamfara ke samu a ɓangaren ilimi. Sanarwar ta ƙara da cewa yawancin ɗaliban da suka fi samun nasara na makarantun gwamnati ne.

Karanta Wannan  Muna da Hujjojin cewa kun aikata laifin cin amanar kasa amma dai Tausayine yasa muka yafe muku>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa kananan yaran da ta yiwa Afuwa

“Wannan nasarar da kuka samu ta nuna cewa gwamnatinmu na ƙoƙari wajen inganta ilimi,” a cewar Gwamna Dauda Lawal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *