Friday, June 26
Shadow

Gwamnoni sun kai ziyarar jaje zuwa Maiduguri

Gwamnonin wasu jihohin Najeriya sun ziyarci birnin Maiduguri domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa iftila’in ambaliya da ya auka wa birnin.

Gwamnonin da suka ziyarci Maidugurin sun haɗa da na Legas Babajide Sanwo Olu da na Ondo, Lucky Aiyedatiwa da na Adamawa, Umar Fintiri da kuma na Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq.

Gwmanan Legas – wanda ya bayyana ambaliyar a matsayin mummuna – ya ce gwamnonin sun jajanta wa iyalan mutanen da lamarin ya shafa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

”A matsayinmu na al’umma ɗaya yana da muhimmanci mu haɗa kai don samar da agaji da taimaka wa aikin ceto, tare da tabbatar da cewa waɗanda lamarin ya shafa sun samu tallafin da suke buƙata”, in ji Gwamnan Sanwo Olu.

Karanta Wannan  Wallahi ba da wasa nake ba, Soyayyar Matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta kamani, kuma wallahi in tace bata sona ban san yanda zan yi ba>>Inji Matashi dan Tiktok

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *