Wednesday, October 9
Shadow

Shugaba Tinubu ya gana da Sarki Charles na Ingila

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana Sarki Charles na Ingila a fadarsa ta Buckingham da ke birnin Landan.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana ganawar a matsayin ta sirri, wadda ta ƙara nuna alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya.

“Shugabannin sun tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashensu, musamman matsalar sauyin yanayi,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu da Sarki Charles sun tattauna hanyoyin da za su iya yin haɗaka musamman a daidai lokacin da ake shirin taron COP 29 da ke tafe a ƙasar Azerbaijan da kuma taron ƙasashe rainon Ingila wato CHOGM da za a yi a Samoa.

Karanta Wannan  Hotunan Sabon Jirgin Saman Shugaban Kasa Bola Tinubu

Ya ce: “Tinubu ya ƙara nanata ƙudurin Najeriya na yaƙi da matsalolin sauyin yanayi a irin yanayin da zai yi daidai da tsare-tsaren makamashin ƙasar.”

Wannan ne karo na biyu da shugabannin suka gana bayan ganawarsu ta farko a Dubai a taron COP 28 na bara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *