Thursday, January 16
Shadow

Gwamnati za ta fara kama yaran da ke yawo a titunan jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai yi aiki kwashe yaran da ke gararamba a titunan birnin.

Hukumomi sun ce ɗaukar matakin ya zama wajibi kasancewar barin yara ƙanana suna yawo a tituna babbar barazana ce ga tsaro da kuma ci gaba al’umma.

Kwamitin zai kuma bai wa gwamnati shawarar kan yadda za a mayar da yaran garuruwan da suka fito.

Kwamitin ƙarkashin shugabancin kwamandan hukumar Hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai bi diddigi tare da zaƙulo yaran da suke yawo a kwararo da tituna suna kwana a kasuwanni da ƙarƙashin gada a sassan birnin Kano domin samar musu da kyakkyawar makoma da kuma maslahar al’umma.

“Yaran da za mu fara kamawa sune waɗanda suke kamar an zubar da su yawo kan titi, waɗanda ba su da wata makoma, mafi yawansu ba a san daga inda suke ba. Waɗansu ‘yan Kano ne wasu yan wasu jihohin wasu kuma ‘yan wajen ƙasar nan ne ma,” in ji Ɗaurawa

Karanta Wannan  Giya ce dalili na 3 na kamuwa da cutar daji(cancer)

“Wasunsu rayuwa ce ta yi musu tsauri ta gagara suka koma kwana ƙarƙashin gada da gareji da wajen tuburan masu shayi. Irin waɗannan yaran mai girma gwamna ke fatan a kama a tantance na gida da na wajen a san matakin da za a ɗauka a kansu.

“A basu tarbiyya a mayar da su cikin al’umma domin su zama masu amfani ka da su zama barazana ga al’umma,” in ji Malam Aminu Daurawa.

Wannan kwamitin dai ya ƙunshi wasu ƙananan kwamitoci waɗanda za su yi aikin tantance yaran ta fuskar lafiya da sauran bayanai.

Sheik Daurawa ya ce ba za a faɗi yaushe za a fara wannan aiki ba domin ka da waɗanda ake son a taimakawa su tsere a gaza cimma manufar aikin.

Karanta Wannan  Hoto:Wata mata ta kkashe mijinta da Tabarya

“An bamu filin sansanin alhazai da ke kusa da filin jirgin sama, a nan za mu ajiye su tsawon makonni biyu mu tantance su da lafiyarsu da kuma garuruwansu.

“Za a yi aikin nan ne ƙarƙashin kwamiti guda huɗu da za su kammala aikinsu cikin kwana 14 sannan gwamna ya bayyana mataki na gaba,” in ji Malam Aminu Daurawa.

To sai dai ‘yan kungiyoyin da ake aikin kare kananan yara na ganin akwai bukatar gwamnati ta lura da wasu mahimman abubuwa.

Barista Badiha Abdullahi Muaz wadda lauya ce kuma shugabar kungiyar fafutukar kare hakkin kanana yara ‘ya’ya mata ta Rayuwa Development Association RADA, ta mayar da su garuruwansu ba shi ba ne mafita, to she ƙofar da suke kwararowa shi ne mataki mafi muhimmanci.

Karanta Wannan  Gwamnatin Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti

“Ba zan cen a mayar da su gida ba ne, dole a yi musu rijista, kuma gwamnati ka da ta ce za ta ɗauki nauyin yaran nan sai dai ta tallafa musu, domin aikin ba mai ƙarewa ba ne,” in ji Barista Badiha.

Ta nemi a yi tsari a cikin unguwanni mutane su riƙa sanya idanu kan mutanen da suke zuwa suke fita a yankunansu.

Bayanai na cewa akwai dubban yara ƙanana akasari maza suna gararamba cikin datti a titunan jihar Kano, wadanda ake cewa suna kwarara birnin ne daga sassan jihar wasu kuma daga jihohi don neman kuɗi ko karatu amma daga bisani sai su ɓude da yawo ba tare da sanin takamaimai ina suka dosa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *