Wednesday, January 15
Shadow

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi a faɗin jihar a wani mataki na farfaɗo da ɓangaren ilimin jihar.

Yayin da yake jawabi a wani taro da gwamnatin jihar ta shiyya, gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya ce matakin ya zama wajibi domin magance matsalolin da ɓangaren ilimin jihar ke fuskanta.

Gwamnan ya kuma yi kira da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimin jihar su fito su haɗa ƙarfi domin magance matsalolin da suka yi wa ɓangaren ilimin jihar katutu.

”Ina Kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da malamai da iyaye da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma, su haɗa kai, wajen farfaɗo da fannin ilimi, domin ci gaban al’ummarmu”’.

Karanta Wannan  Kalli kwalliyar Sallah ta Nazir Ahmad Sarkin Waka

”Samun ilimi mai inganci shi ne babban makami mafi inganci na yaƙi da talauci da miyagun laifuka cikin al’ummarmu”.

Gwamna ya ce manufar ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi shi ne samar da gagarumin sauyi kan yadda fannin ilimin jihar ya taɓarɓare.

Abba Kabir ya ce matakin zai bai wa gwamnati damar yin shiri domin aiwatar da gyare-gyare cikin gaggawa da mai da hankali wajen lalubo dabarun da za su sake gina ɓangaren ilimin jihar.

”Matakin zai taimaka wajen ceto makarantunmu da suka durƙushe, mataki ne mai tsauri na tabbatar da cewa kowane yaro a jihar Kano ya samu ilimi mai inganci, wanda shi ne babban hakkinsu”, in ji gwamnan.

Karanta Wannan  Mexico ta zaɓi mace ta farko shugabar ƙasa

Gwamnan ya kuma ce wannan mataki zai taimaka wajen kawar da duk yaran da ba su zuwa makaranta daga titunan jihar domin mayar da shu makarantu.

”Domin cimma wannan, da farko, dole mu samar da azuzuwa domin yara kimanin 989,234, da ba sa zuwa makaranta a cikin Jiharmu, Za mu gina azuzuwa 28,264 nan da shekaru 3 masu zuwa a fadin jihar”.

”Ma’aikatar ilimi da SUBEB za su sa ido kan yadda za a gudanar da ayyukan”.

”Domin daƙile matsalar rashin malamai, musamman a makarantu 400 da ke shiyyar Kano ta Kudu, inda ake samun malamai ɗaya a kowace makaranta, mun bayar da umarnin bai wa malaman BESDA 5632 takardun ɗaukar aiki na dindindin da za su fara daga yau”, in Abba Kabir.

Karanta Wannan  Da Ɗuminsa: Ba Za Mu Tafi Yajin aiki ba – NLC ta bayyana

”Haka kuma, mu bayar da dama wajen ɗaukar ƙarin malaman makaranta 10,000”,

Gwamnan ya ce ya bai wa SUBEB damar tsara yadda za ta gudanar aikin horas da malaman makarantar a faɗin jihar.

Abba Kabir Yusuf ya ce malaman makaranta za su ci gaba da samun horo lokaci zuwa lokaci don cimma burin da gwamnatin ta sanya a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *