
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe Naira Biliyan 1 da Miliyan 6, domin auren zawarawa karo na biyu.
Kwamishin yaɗa labarai da harkokin cikin gida Kwamarad Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai kan sakamakon zaman majalisar zartaswar jihar Karo na 32 da ka gudanar ranar juma’ar da ta gabata.
Me zaku ce?