Monday, December 16
Shadow

Gwamnatin Najeriya ta roƙi ‘yan ƙwadago su janye yajin aiki

Gwamnatin Najeriya ta roƙi haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta ‘yan kasuwa TUC da su janye yajin aikin da suka fara a yau Litinin.

Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya nemi ‘yan ƙwadagon su koma kan teburin tattaunawa, kuma bayanai sun nuna cewa yanzu haka ma ‘yan ƙwadagon na tattaunawa da wakilan gwamnatin a Abuja.

“Wannan roƙo ne muke yi cikin sanyin murya ga ƙungiyoyin ƙwadago da su dawo teburin tattaunawa da gwamnatin Najeriya da na jihohi ƙarƙashin jagorancin kwamatin lalubo mafi ƙarancin albashi,” in ji ministan yayin wani taron manema labarai.

A matsayinmu na gwamnati, muna muradin a cimma matsaya cikin lumana kuma za mu yi duk mai yiwuwa wajen cimma hakan. Jiya shugabannin majalisa sun gana da ‘yan ƙwadago, yau mu ma mun sake gayyatar su don cigaba da tattaunawar.”

Karanta Wannan  Hotuna da Bidiyo: Kalli yanda wasu 'yan Afrika ke tafiya a kafa a Sahara a kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turawa

Ministan ya sake jaddada cewa adadin kuɗin da NLC da TUC ke nema na N494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi “ba mai yiwuwa ba ne” kuma “zai iya gurgunta tattalin arzikin ƙasa da jawo rasa ayyukan yi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *