Sunday, March 16
Shadow

Gwamnatin Shugaba Tinubu na shirin karbi bashi har sau shidda daga bankin Duniya a wannan shekarar

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin karbo bashi har sau shidda daga bankin Duniya da jimullar kudin suka kai Dala Biliyan $2.23 a wannan shekarar da muke ciki ta 2025.

Bayanai daga bankin Duniyar ya nuna cewa hakan zai kawo yawan kudaden da Bankin ya baiwa Najeriya bashi zuwa jimullar Dala Biliyan $9.25 a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Hakan na kara nuni da yanda Najeriya ke dogaro da bashi wajan gudanar da ayyukan Gwammati.

Rahotanni sun bayyana cewa, a mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu an samu karin yawan bashin da ake bin Najeriya, wanda ko da a shekarar data gabata, shugaban ya ciwo bashi sosai.

Karanta Wannan  An kama matashi dan shekaru 19 da ya kàshè dansa me kwana 3 a jihar Adamawa

Hakan na zuwane duk da kiran da shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajaero yayi ga bankin Duniyar na cewa su daina baiwa shuwagabannin kasashe Irin Najeriya bashi saboda ba al’umma akewa aiki da kudaden ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *