
Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane dan karbar kudin Fansa su biyu a Barkin Ladi dake Jihar Plateau.
Rahoton yace an kama su ne bayan da wasu da aka kama a baya suka bayar da bayanai akan maboyarsu. Kuma an kamasu ne a kauyen Lugere Sho.
Hakanan an kara kama wani me garkuwa da mutanen a Kauyen Kwok duk dai a Barkin Ladi kuma yana bayar da bayanai game da ta’asar da yayi a baya ciki hadda garkuwa da mutane a jiharta Filato da Nasarawa.
Hakanan ya bayar da bayanai akan wadanda suke aiki tare da maboyarsu inda jami’an tsaro tuni suka bazama dan nemosu.