
Gwamnatin Tarayya na barazanar korar ma’aikata, 3,598 da suka ki yin tantancewa daga aiki.
Gwamnatin tace idan aka sake yin tantancewar, duk wanda bai yadda an tantanceshi ba, za’a dauka kawai takardat daukar aiki ta boge gareshi.
Za’a yi tantancewarce daga ranar 18 ga watan Augusta zuwa ranar 28 ga watan a ma’aikatu daban-daban na tarayya.
An bukaci ma’aikatan dasu gabatar da takardun daukarsu aiki dana karin girma da sauransu.