Friday, February 13
Shadow

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kudi Naira Miliyan Dubu Domin Gina Makarantar Horar Da ‘Yan Sanda A Garin Kafin Hausa Dake Jigawa

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Sanata Abdulhamid Ahmed Malam Madori, ne ya bayyana haka yayin taron gwamnati da jama-a a Kafin Hausa.

Ya ce an sanya kudin a cikin kasafin kudin 2025, kuma majalisar dattawa ta riga ta amince da dokar kafa makarantar wadda ake jiran sa hannun shugaban kasa.

Sanata Malam Madori ya bayyana cewa shi ne ya dauki nauyin gabatar da kudurin kafa makarantar wadda za ta taimaka wajen samar da kwararrun ‘yan sanda na zamani domin inganta harkar tsaro a fadin kasar nan.

Ya nuna cewa ya riga ya bai wa ofishin ‘yan sanda na Kafin Hausa sabuwar motar Hilux tare da gyara da samar da kayayyaki ga ofishin da gidajen ‘yan sanda, domin karfafa gwiwar jami’an da ke aiki a yankin. Bugu da kari, ya tallafa wa matasa da mata sama da 8,000 a Kafin Hausa, yayinda ya bayar da fiye da Naira miliyan 5 don kammala babban masallacin Juma’a a gari.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya zata baiwa kananan 'yan kasuwa da suka yi zarra Kyautar Naira Miliyan 220, duba rabar da za'a fara rijista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *