Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana baiwa masu boye da dalar Amurka a gidaje su fito da ita su kai banki wata tara.
Gwamnatin tace idandai kudaden na halas ne ba na sata ba ko zamba cikin aminci ba,babu wani hukunci da za’a wa mutum idan ya fito dasu.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka inda ya zargi cewa masu boye dalar na taimakawa wajan kara karancinta da tsadarta a Najeriya.