
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 23.35 dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna.
Gwamnatin ta saka hannu ta karbo bashin a madadin gwamnatin jihar Kaduna wanda wannan na daga shirin ciwo bashin Dala Miliyan $62.8m dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar.
Daraktan yada labarai na ma’aikatar kudi ta tarayya, Mohammed Manga ya tabbatar da hakan inda yace za’a yi amfani da wannan kudi dan inganta karatun akalla yara 100,000.
Sannan za’a yi amfani da kudin wajan gyaran makarantu da sauran abubuwan da suka shafi harkar ilimi a jihar.