Friday, December 12
Shadow

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan Ķudin CCT/RRR 25K Ta Hanyar Biya Ķai Tsaye

Shiga Shafin hutudole na WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan Ķudin CCT/RRR 25K Ta Hanyar Biya Ķai Tsaye

Ana biyan ne ga wadanda aka yi musu updating na imformation dinsu, sannan biyan NASSCO ta hanyar ATM na cigaba da tafiya shima.

Bankunan da aka fara biya sune UBA, FCMB, FIRST BANK da ECO. Sune na rukunin farko na fara biyan wato (First batch A) payment.

Har yanzu ana cigaba da sabunta bayanan dama shigar da bayanan wadanda suka nema tun lokacin mulkin Buhari, idan ba ku sabunta bayanan ku ba za ku iya rashin rabauta da samun wannan tallafin na gwamnatin tarayyar Nijeriya.

Karanta Wannan  Yayin da aka fara zàngà-zàngà, farashin kayan abinci ya sake tashi

Shi dai wannan biyan tun farkon mulkin shugaban Tinubu aka fara biya sai aka dakatar da biyan sakamakon wasu badakaloli da ake zargin wasu kusoshin gwamnatin da tafkawa a shirin, amma yanzu biyan a wannan shekarar ya cigaba kamar yadda Ministar Jinkai da walwalwa ya shaidawa Ambasada na bankin duniya biyan zai cigaba wannan watan.

Kuna iya zuwa gundumarku na karamar hukumarku domin sabunta muku ko kuma
idan kuna bukatar a sabunta muku bayananku, kuna iya tuntubar mu ta wannan lambar wayarmu wadda da muke watsapp da ita kawai; 09032914890

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *