Sunday, March 16
Shadow

Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan Tituna a duk fadin Najeriya

A shirye-shiryen bukukuwan karshen shekara, Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan titunan kasarnan.

Hukumar dake kula da titunan Najeriya, FERMA ce dai ta ke kula da gyaran.

Shugaban hukumar, Engr. Chukwuemeka Agbasi ne ya kaddamar da fara gyaran titunan a jihar Kano.

Yace za’a yi wadannan kyaran ne dan samarwa mutane saukin ziyara da komawa garuruwansu dan yin bukukuwan karshen shekara.

Yace sun gano titunan da aka fi amfani dasu kuma sune zasu fi baiwa fifiko a wajan gyaran.

Ya bayyana cewa, wannan aiki zai samarwa da mutane akalla 12,000 abin yi wanda hakan zai habaka tattalin arzikin kasa.

Karanta Wannan  'Yan kasuwar man fetur zasu shigo da man fetur daga kasashen waje wanda yafi na Dangote Sauki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *