Rahotanni daga jihar Borno na cewa a can ma an gurfanar da kananan yara a kotu bisa zargin shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da daga tutar Rasha.
Wadanda aka gabatar din su 19 ne wanda cikinsu akwai guda 3 wanda kananan yara ne.
Wannan na zuwane bayan da aka yi shigen irin hakan a babban birnin tarayya, Abuja.
Mai Shari’a, Justice Aisha Mohammed Ali ce ta jagoranci zaman kotun kuma kananan yaran da aka gabatar a gabanta suna da shekaru 14 ne zuwa 15.
Babbar Lauya a jihar ta Borno, Hauwa Abubakar ce ta gabatar da karan inda ta zargi wadanda aka gurfanar da batawa Gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum suna da kuma tunzura mutane su yiwa gwamnati bore da kuma shirin daukar makamai.
Hakanan wasu daga cikinsu an zargesu da daga tutar Rasha.
Duka dai sun musanta zargin da ake musu inda lauya me gabatar da kara yace a bashi lokaci dan ya gabatarwa da kotu shaidu.
Shi kuma lauyan dake kare wadanda ake karar, Barrister Yakubu Alhaji Adamu ya nemi kotu ta saka ranar da za’a dawo a ci gaba da wanna Shari’a nan kusa musamman lura da cewa an tsare wadanda ake zargin har na tsawon sama da kwanaki 90, yace ta hanyar gaggauta shari’ar ne kawai wadanda ake zargin zasu samu hukunci na gaskiya.
Mai Shari’a ta daga ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba inda ta bukaci yaran a kaisu inda ake tsare yara na musamman su kuma manyan a kaisu gidan yari.