Wednesday, January 15
Shadow

Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar kwadago, NLC ta dawo a ci gaba da tattaunawa game da mafi karancin Albashi

A jiya Laraba, wasu majiyoyi sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar Kwadago ta dawo a ci gaba da tattaunawa kan maganar mafi karancin Albashi.

A zama na karshe dai an tashi baram-baram bayan da NLC din taki amincewa da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi.

Hakanan wata majiyar tace kungiyar kwadagon ta amince da cewa zata amsa gayyatar ta gwamnati.

Kungiyar dai ta baiwa Gwamnati nan da karshen watan Mayu da muke ciki a gama maganar mafi karancin Albashin ko kuma ta tafi yajin aiki.

Karanta Wannan  Farashin Naira zai tsaya akan 1,450 akan kowace dala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *