Gwamnatin tarayya karkashin Ma’aikatar mata ta haramtawa Kananan yara ‘yan kasa da shekaru 18 shiga otal.
Ministar matan, Uju Ohaneye ce ta bayyana hakan inda tace dole duka otal din dake Najeriya dolene su bi wannan umarni.
Tace duk Otal din da aka samu bai bi wannan umarni ba zai iya fuskantar hukuncin dakatarwa.
Tace an dauki matakanne dan kawar da matsalar safarar ‘yan mata.
Hakan na zuwane dai a yayin da wasu bidiyon ‘yan mata dake da shekarun tsakanin 15 zuwa 16 aka ga an yi safarar su zuwa kasar Ghana dan yin Karuwanci.
[…] Ama kan hakane Gwamnatin ta yi sabuwar dokar da ta hana zuwan kananan ‘yan mata da basu cika shekaru 18 ba zu… […]