Gwamnatin tarayya ta kara yawan kudin ciyar da masu laifi a gidan gyara hali wanda aka fi sani da gidan yari a kasarnan daga Naita 750 zuwa Naira 1,125 a kullun
A baya dai da ake ciyar da ‘yan gidan yarin akan Naira 750 a kullun, ana cire kudin haraji da sauransu wanda a karshe Naira 500 ce take raguwa a matsayin abinda za’a ciyar da ‘yan gidan yarin sau uku a rana.
Shugaban gidajen gyara hali na Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche ne ya bayyana haka a wani taro da yayi da jami’an hukumar kula da gidan gyara halin.
Ya sha Alwashin ci gaba da neman inganta rayuwar masu laifi da ake tsare dasu.