Gwamnatin tarayya ta sanar da kashe Naira Biliyan 1.4 wajan canjawa masu tsatstsauran ra’ayi irin su B0K0 Hàràm tunani.
Hakan ya farune a cikin shekara daya da rabi data gabata inda aka kafa sansanonin canjawa masu tsatstsauran ra’ayi da suka tuba tunani.
A ranar May 12, 2022 ne tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanyawa kudirin dokar kafa cibiyar yaki da ayyukan ta’addanci a Najeriya wanda kuma a karkashinta ne ake kula da tubabbun ‘yan Boko Haram din.
Gwamnatin tarayya dai ta gina cibiyoyin kula da irin wadannan mutane da suka tuba daga ayyukan ta’addanci.