Wednesday, January 15
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta kwace aikin gyara titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano daga hannun kamfanin Julius Berger

Gwamnatin tarayya ta kwace aikin gyaran Titin Abuja zuwa Kaduna, zuwa Zaria, zuwa Kano daga hannin kamfanin Julius Berger Plc.

Sanarwar hakan ta fito ne daga ma’aikatar ayyuka ta tarayya kuma dalilin hakabya biyo bayan rashin samun matsaya tsakanin kamfanin na Julius Berger da Gwamnatin tarayya akan kudin aikin yanda za’a ci gaba da gudanar dashi.

Kamfanin dai na Julius Berger yaki aiwatar da umarnin Gwamnatin tarayyar na ci gaba da aikin gyaran Titin inda ya kwashe ma’aikatansa daga kanntitunan.

Tun zuwan Gwamnatin Tinubu,ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta kwase watanni 13 tana kokarin sasantawa da kamfanin akan yanda za’a ci gaba da aikin amma abu yaci tura.

Karanta Wannan  Ta leko ta Koma, Ji sabuwar wakar da Rarara ya saki bayan hukuncin kotu

Dalilin hakane gwamnatin tace ta kwace kwangilar gina titin daga hannun Kamfanin kuma ya kwashe kayansa ya kara gaba.

A shekarar 2018 ne dai gwamnatin tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta baiwa kamfanin na Julius Berger aikin gyaran titin inda a yanzu an kamma aikin Titin Kaduna zuwa Zaria inda na Kano zuwa Zaria saura kadan amma na Abuja zuwa Kaduna kaso 27 cikin 100 ne kawai aka kammala.

Hakanan bayan zuwan Gwamnatin Tinubu an raba aikin gida biyu inda aka baiwa kamfanin Dangote wani sashe dan ci gaba da gyaran wanda ake ginawa da siminti amma kamfanin Julius Berger ba’a samu matsaya dashi ba.

Karanta Wannan  Bidiyo: Kalli Yanda Sojan Ruwa wanda matarsa taje Berekete Family akan an daureshi yaki bayar da Bindigar sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *