Gwamnatin tarayya ta musanta ikirarin lauyanta da yace wadanda aka kai gaban kotu a Abuja ba yara bane.
idan dai ba’a mantaba a baya lauyan gwamnatin yace wasu ma daga cikin wadanda aka gurfanar na da aure wasu sun kammala jami’an, lamarin da ya jawo cece-kuce.
Saidai a sabuwar sanarwar da ministan yada labarai, Mohammed Idris ya fitar yace shugaba Tinubu yace a dakatar da duk wata shari’a da ake akan yaran a sakesu.
Sannan kuma yace dukansu yarane.
Yace za’a binciki duka jami’an tsaron dake da hannu a lamarin dan ganin ko akwai wanda ya aikata ba daidai ba dan a hukuntashi.
Sannan shugaban kasar ya bayar da umarnin kula da yaran da kuma mikasu hannun iyayensu da masu kula dasu cikin aminci.