
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta mikawa Bankin Duniya bukatar ciwo sabon Bashin dala Biliyan $1.5.
Hakan na zuwane yayin da bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira Tiriliyan N166.79tn.
A bukatar da gwamnatin ta mikawa Bankin Duniya, Najeriya tace tana neman bashinne dan bayar da tallafi ga talakawa marasa karfi da kuma Taimakawa Fannin Noma.
Bashin dai Gwamnatin ta bukaci dala Miliyan $500 ne har sau 3.