Monday, September 28
Shadow

Tawagar Me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar siyasa, Ibrahim Masari ta yi Hadari

Rahotanni sun bayyana cewa, Tawagar me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar siyasa, Ibrahim Masari ta yi hadari.

Hadarin ya farune a karamar Hukumar Kafur ta jihar yayin da ya je yin wata gaisuwa.

Rahoton yace mutane 2 sun rigamu gidan gaskiya.

Hadimin Ibrahim Masarin me amfani da sunan Wazirin Kabir Ibrahim Masari ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook kamar haka:

“Innalillahi wa’innailaihir raju’u😭😭 Acikin tawagar da suka raka Alh Ibrahim Masari Ta’aziyya Dantitture Yanzu nan ansamu Hatsarin mota wasu sun rasu mutum 2 munkawo wata asibiti

Allah ya jiqansu da rahama, su Kuma masu rauni Allah ya basu lapia.”

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Gfresh Al-amin ya koma gidansa ya tarar matarsa ta rufe mai gida, Yace Tana ta babatun wai Ta auri dan Bariki, Yace tunda ya aureta bai taba kwana a waje ba

Da fatan Allah ya jikansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *