Thursday, May 15
Shadow

Gwamnatin tarayya ta samu Naira Biliyan 84 daga kudin harajin Naira 50 da take cirewa akan duk Dubu 10 da ‘yan Najeriya suke fire daga Bankinsu

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Gwamnatin tarayya ta samu jimullar Naira Biliyan 84.03 daga kudin harajin Naira 50 da aka sanya akan kowace Naira Dubu 10 da ‘yan Najeriya suka cire daga bankinsu.

An samu wadannan kudade ne a cikin watanni 3 na farkon shekarar nan da muke ciki.

A watanni 3 na farko na shekarar data gabata ta 2024, kudaden shigar da aka samu ta irin wannan hanya Naira Biliyan N47.74bn ne wanda hakan ke nuna a yanzu an samu karin kaso 76 cikin 100.

Wadannan kudade ana rabawa gwamnatoci ne a matakai daban-daban watau gwamnatin tarayya dana jihohi da kananan hukumomi.

Karanta Wannan  Akwai yiwuwar Man United ta koma ƙasan teburi - Amorim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *