Thursday, September 3
Shadow

Gyare-Gyaren da muka yi akwai wahala, amma suna bada sakamako me kyau>>Inji Gwamnatin Tarayya

Gwamnan babban Bankin Najeriya, Cardoso ya bayyana cewa, Gyare-Gyaren da gwamnatin tarayya ta zo dasu babu sauki amma suna bayar da sakamako me kyau.

Ya bayyana hakane a wajan taron da aka gudanar a birnin Washington DC na kasar Amurka wanda IMF da bankin Duniya suka shirya.

Yace wadannan Gyare-Gyaren sun dora Najeriya a turbar ci gaba kuma a yanzu suna bayar da sakamako me kyau.

Wasu daga cikin Gyare-Gyaren da gwamnatin tarayya ta kawo sune cire tallafin man fetur, cire tallafin dala da sauransu.

Karanta Wannan  'Yan Kudu, Musamman Inyamurai na cewa, Kalaman rashin kyautawa da me magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga yayi akan Buhari tun kamin a Binneshi da sanin Tinubu yayi su, Hakan na zuwane duk da Bayo Onanuga ya goge kalam nasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *