Thursday, January 15
Shadow

Gwamnatin Tarayya tace ba zata iya gano inda Tshàgyèràn Dhàjì masu nuna kudi da màkàmàì a Tiktok suke ba

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ba zata iya bibiyar inda tshageran Dhajin masu nuna kudi da makamai a Tiktok suke ba.

Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi a gidan Rediyo me suna Nigerian Info.

Yace duk wani me amfani da yanar gizo a fadin Najeriya sun san inda yake zasu iya bibiya da zuwa inda yake dan a kamashi.

Yace amma su tshageran Dhajin suna amfani da manhajar yanar gizo ta Starlink ce wadda gwamnati bata iya bibiyarta shiyasa.

Karanta Wannan  Duk Wanda Yake Son Shigowa Jam'iyyar APC A Kano To Kofa A Bude Take Da Ya Shigo, Amma Mutum Ya Sani Duk Kyawun Dan Amarya Sunansa Agola, Inji Hon Alhassan Ado Doguwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *