Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa zata saka karuwanci a matsayin daya daga cikin alkaluman da take amfani dasu wajan tantance karfin tattalin arzikin Najeriya
Hakanan bayan karuwancin, za’a kuma saka harkar kwaya a cikin hanyoyin da ake samarwa gwamnati kudi da kara karfin tattalin arziki.
Shugaban hukumar, Dr. Baba Madu ne ya tabbatar da hakan i da yace akwai kasashen da kwaya ce babbar hanyar samun kudin shigarsu sannan akwai wanda kuma ke karuwanci kuma suna samun kudi fiye ma da masu aikin yi.
Yace duka wadannan za’a sakasu a cikin masu taimakawa karfin tattalin arzikin Najeriya.