Friday, January 17
Shadow

Gwamnatin tarayya tace zata saka karuwanci cikin hanyar samun kudin dake karawa tattalin arzikin Najeriya karfi

Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa zata saka karuwanci a matsayin daya daga cikin alkaluman da take amfani dasu wajan tantance karfin tattalin arzikin Najeriya

Hakanan bayan karuwancin, za’a kuma saka harkar kwaya a cikin hanyoyin da ake samarwa gwamnati kudi da kara karfin tattalin arziki.

Shugaban hukumar, Dr. Baba Madu ne ya tabbatar da hakan i da yace akwai kasashen da kwaya ce babbar hanyar samun kudin shigarsu sannan akwai wanda kuma ke karuwanci kuma suna samun kudi fiye ma da masu aikin yi.

Yace duka wadannan za’a sakasu a cikin masu taimakawa karfin tattalin arzikin Najeriya.

Karanta Wannan  Ji yanda ta kaya bayan da Sanata ya cewa daya daga cikin ministocin da suke tantancewa tana da kyau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *