Saturday, December 28
Shadow

‘Gwamnatin tarayya za ta yi cikakken bincike kan harin ƙauyukan Silame’

Gwamnatain tarayya ta alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtawa a ƙaramar hukumar Sileme da ke jihar Sokoto.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, gwamnan jihar Ahmad Aliyu, ya ce ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Bello Matawalle ne ya tabbatar da hakan a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar ranar Juma’a.

A ranar 25 gatan Disamba ne wani hari da jiragen sojin Najeriya suka ”kai wa Lakurawa” ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10 a ƙauyukan.

”Gwamnatin tarayya ta tabbatar mana cewa za ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa lamarin domin yi wa waɗanda lamarin ya shafa adalci”, kamar yadda gwamnan ya wallafa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Motocin dakon man fetur sun fara jigilar man daga matatar Dangote

Tuni dai rundunar sojin ƙasar ta musanta hannu a kisan fararen hulan, inda ta ce bama-baman da Lakurawa suka ɓoye ne suka fashe bayan harin nasu, lamarin da ya yi nadiyyar mutuwar mutanen 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *