Thursday, September 24
Shadow

Kasar Nijar ta koro karin ‘yan Najeriya 392 zuwa gida

Kasa da mako daya bayan da kasar Nijar ta dawo da ‘yan Najeriya su 310 zuwa gida Najeriya, kasar ta sake taso keyar wasu karin mutane 392 zuwa Najeriya.

Hakan ya kawo jimullar ‘yan Najeriya da aka dawo dasu gida daga kasar Nijar zuwa 702 a cikin sati daya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a lamarinne suka tarbi ‘yan Najeriyar da aka koro daga Nijar a Titin Airport Road dake Kano.

Hukumar ta NEMA ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na X.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Mahaifina me Arziki ne kuma nima 'yar kasuwace amma duk wanda ya fito yana sona ba dan Allah yake zuwa ba sai dan Dukiyar mahaifina, Shine nake neman me sona na gaskiya ko da talakane>>Inji Wannan matashiyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *