
Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta rabawa ‘yan Najeriya Miliyan 8.8 tallafi dan rage musu radadin talauci.
Gwamnatin tace zata raba wannan tallafi ne a mazabun dakw fadin kasarnan da suka kai 8,809.
A ranar Alhamis ne gwamnatin ta sanar da wannan shiri sannan tace za’a gudanar dashi ne a karkashin ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki.
Gwamnatin tarayyar tace, Kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta karfafa mata gwiwa wajan aiwatar da wannan aiki.