Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin kasafin kudi.
Gwamnatin zata ciwo bashinne a wannan shekarar ta 2024 kuma zata yi hakan ne dan samar da kudin da zata biya tallafin man fetur wanda zai lakume Naira Tiriliyan 5.4.
Kafar yada labarai ta Reuters ce ta ruwaito wannan labari.
Saidai Gwamnatin tarayya ta ci gaba da nanata cewa ita fa har yanzu bata biyan tallafin man fetur.