Karamin ministan man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayar da umarni a fara sayar da man fetur a sama da Naira Dubu daya watau sama da farashin da ake dauka a Depot wanda Naira 1117 ne.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro a Abuja.
Yace ta hakane kawai za’a hana masu fitar da man fetur zuwa kasashen waje daga Najeriya.
Ya kuma zargi jami’an tsaro da hannu wajan taimakawa masu safarar man fetur din daga Najeriya zuwa wasu kasashe alhalin ‘yan Najeriya ne aka yi tallafi dominsu.