
Kungiyar gwamnonin PDP sun sha Alwashin kai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kara a kotu saboda dakatar da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara inda ya kakaba dokar ta baci a jihar.
A sanarwar da suka fitar ta bakin Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, PDP sun ce shugaba Tinubu ya amince yayi kuskure sannan ya mayar da Fubara kan kujerarsa ta gwamna.
Gwamnonin na PDP sun zargi shugaban kasar da nuna bangaranci wajan daukar wannan mataki inda suka ce yaki ya bayyana kuskuren Ministan Abuja, Nyesome Wike wajan jefa jihar ta Rivers a halin data tsinci kanta.
Kungiyar gwamnonin tace tana tare da mutanen jihar Rivers a wannan tsaka mai wuya da suka tsinci kansu, sannan sunce auna tare da kungiyar Lauyoyin Najeriya, NBA da tace wannan mataki ya sabawa doka.
Kungiyar Gwamnonin tace shugaban kasar yayi gaggawa wajan daukar wannan mataki.