
Daya daga cikin hadiman tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana damuwarsa kan salon shugabancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ana fifita yankin Legas da Kudu maso Yamma fiye da sauran sassan kasar.
A wani rubutu na ra’ayi da ya wallafa a yau Asabar, Yakasai ya ce ko da ya ke ya fahimci taken “Emi Lokan” da Shugaba Tinubu ya yi amfani da shi a lokacin kamfen din sa, yana yawan tambayar ko shugaban Najeriya ne gaba ɗaya ko kuma na Legas kawai.
“Ana nuna wariya idan aka kwatanta da Legas, ba kawai a fannin ayyuka ba har ma da na mukamai,” in ji Yakasai. “Zai yi kyau mu ce ‘Emi Lokan’ ta rikide zuwa ‘Lagos Lokan’.”
Yakasai ya bayyana damuwa kan abin da Najeriya za ta fuskanta idan wannan tsarin da ake gani a yanzu ya ci gaba har zuwa shekara ta 2031. Ya ce ba kawai aikin gwamnati ake bukata ba, amma adalci, daidaito, da gaskiya su ne ginshikin shugabanci nagari.
Ya kara da cewa duk wani dan Legas mai kishin kasa da hangen nesa zai gane cewa irin wannan fifiko da ake bai wa Legas abin kunya ne da ba a taba gani ba a tarihin kasar.
A karshe, Yakasai ya ce ko da wasu za su ci gaba da kare manufar siyasa a ko wane hali, su kuwa za su ci gaba da fadin gaskiya domin tarihi ya rubuta abin da ya dace ga al’ummar da ke zuwa.