Kurkur na daya daga cikin muhimman abubuwan dake gyara fuska sosai ta yi tas babu kuraje ko duhu ko rauni.
A wannan rubutun, zamu kawo muku amfanin da Kurkur kewa fuska da kuma yanda za’a yi amfani dashi.
Ana hada Kurkur da dichloromethane, wanda za’a iya samunsa a Kemis da yawa dan maganin duhu da dattin fuska.
Hakanan ana hada Kurkur da gyada, Gotu Kola inda suke maganin:
Kumburin Fuska.
Kaikayin fuska.
Da maganin duhu da dattin fuska.
Hakanan ana hada Kurkur da Gotu Kola da Rosemary inda suke maganin alamun tsufa dake bayyana a fuska. Dan samun sakamako me kyau a yi sati 4 ana amfani dasu.
Hakanan ana amfani da Kurkur wajan gyara tabon ciwo a fuska.
A takaice idan duk ba’a samu abubuwan da muka bayyana a sama ba, ana hada Kurkur da Yoghurt ko zuma a kwaba a shafa a fuska dan maganin matsalolin fuska.
[…] Hakanan ana amfani da Kurkur wajan cire tabon fuska, yanda ake yi shine ana hada Kurkur da Yoghurt ko Zuma a kwaba a shafa a fuska. Mun yi cikakken bayani yanda ake amfani da Kurkur wajan gyaran fuska. […]