Wednesday, January 15
Shadow

Gyaran fuska da kwai

Ana amfani da kwai wajan gyaran fuska sosai dan magance matsalolin da kan iya shafar fuska.

Ga hanyoyin da ake amfani da kwan kamar haka:

Ana fasa kwan a cire kwaiduwar a bar ruwan kwan kawai sai a hada da zuma, da ruwan lemun tsami ai ta bugawa har sai sun hadu.

Idan ya hadu sosai sai a wanke fuska da ruwan dumi.

A fara shafawa a hannu adan barshi zuwa mintuna biyar, idan ba’a ga wata matsala ba, daga nan sai a shafa a fuska,dalilin yin hakan shine wasu yana musu reaction.

A barshi ya kai mintuna 10 zuwa 15 a fuska? Daga nan sai a wanke.

Ana iya yin hakan sau 3 a mako.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da ayaba

Wannan hadi yana sa fatar fuska ta yi laushi ta yi kyau sosai? Yana maganin kurajen fuska da kawar da tattarewar fuska da kuma maganin tsufan fuska.

Sannan kuma ana yin hadin Ruwan kwai, Shima a cire kwaiduwar a bar farin ruwan kwai a zuba Yoghurt baban cokali 1 a juya.

A shafa a fuska na tsawon mintuna 10 zuwa 15.

Yana maganin kurajen fuska da matacciyar fatar fuska me sa fata duhu, da sauran matsalolin fata.

Hakanan akwai hadin da ake hadawa na farin ruwan kwai ba tare da Gwaiduwa ba da kurkur. Ana juyawa sosai dan hadin ya hadu.

Bayan hadawa, ana shafawa a fuska zuwa mintuna 15.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da haske

Yana batar da tabon fuska, Yana kuma dawo da ainahin kalar fatar fusks.

1 Comment

  • […] Ana kuma amfani da Farin ruwan Kwai wajan kawar da tabon fuska, yanda ake yi shine, Ana fasa kwai a cire gwaiduwar a bar farin ruwan a hada da zuma ko kurkur a juya sosai a rika shafawa a fuska, mun yi bayani kan yanda ake amfani da farin ruwan kwai wajan gyaran fuska. […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *