Bayan Amfani a Miya, Tumatir na da wani amfani musamman a wajan gyaran fata da fuska:
Ga amfanin da yakewa fuska kamar haka:
Tumatur na daidaita man fuska.
Idan ya kasance fuskarki me yawan samar da maski ne ko mai wanda bata barin kwalliya ta dade a jikin fuskar, kina iya amfani da tumatur wajan maganin wannan matsala.
Yanda ake yi shine:
Zaki dauki tumatur ki yankashi gida biyu.
Sai ki shafashi akan fuskarki.
Ki barshi yayi mintuna 10 akai sannan ki wanke da ruwa.
Yin hakan akai-akai zai yi miki maganin yawan maikon fuska.
Za’a iya yin Amfani da Tumatur dan kawar da dattin da ya makale a fuska wanda wanki da sabulu baya masa.
Akwai abubuwa da yawa irin su dattin masana’antu da sauransu wanda idan suka hau kan fata ko fuska, dan wanka ko wankewa da ruwa baya fitar dasu? Hakan zai iya sawa fuskar mutum ta yi duhu.
Dan haka ana iya amfani da Tumatur zalla ba da hadin komai ba, wasu na hadawa da Sikari/Sugar amma hakan na iya yiwa fata Illa.
Dan haka a shafa tumatur zalla a barshi minti Goma a wanke.
Tumatur na maganin Kurajen Fuska.
Kurajen fuska dake batawa musamman ‘yan mata fuska ta yi ba kyan gani ana iya amfani da Tumatur dan magance wannan matsala.
Ana samun ruwan tumatur a hada da Tea tree essential oil a shafa a fuska.
A barshi yayi mintuna 15 zuwa 30 sai a wanke.
Ana iya yin hakan sau 2 a sati dan samun sakamako me kyau.
Tumatur na sa hasken fata, ainahin kalar fatar mutum zata fito.
Ana amfani da ruwan Tumatur da Kurkur a hada da itacen sandalwood, ko kuma ince irin itacennan da ake hada turaren wuta dasu, ana hadasu a daka a yi kamar fate ko markade.
Ana shafawa a fuska a barshi ya bushe.
Bayan ya bushe sai a wanke.
Za’a ga abin mamaki.
Idana ana fama da kaikayin fata ko fata tana bori ko ta yi jaa haka kawai ana amfani da Tumatur wajan magance wannan matsala.
Yanda ake yi shine za’a matse ruwan tumatur a hada da ruwan gurji a shafa a fuska.
Ana barinshi daga mintuna 15 zuwa 20 sai a wanke.
A maimaita har sai an samu sauki.
Ana amfani da tumatur dan maganin tattarewar fuska:
Idan fuska ta fara nuna alamar tsufa da kuma duhu na yawan shekaru ana iya magance hakan da tumatur.
Ana amfani da ruwan tumatur a hada da Avocado a shafa a fuska.
A bari ya fara bushewa sai a wanke.