Wednesday, October 9
Shadow

Gyaran gashi da aloe vera

Aloe Vera nada amfani sosai a gashi. A wannan rubutun zamu yi bayanin yanda ake amfani dashi dan gyaran gashi.

Kara Tsawon Gashi: Aloe Vera na da sinadaran vitamins A, B12, C, da E da kuma Fatty Acids da Amino Acids wanda ke taimakawa sosai wajan kara tsawon gashi.

Aloe Vera na kuma maganin kaikayin kai da Dandruff ko Amosanin kai, daduk sauran matsalolin dake sa gashi ko kai kaikayi.

Hakanan kuma Aloe Vera na maganin illar da rana kewa gashi ta hanashi sheki da canja kala kakkaryewa.

Aloe Vera bashi da illa sosai idan aka yi amfani dashi a gashi dan hakane masana suka ce abune wanda za’a iya amfani dashi kai tsaye.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da tafarnuwa

Dan samun sakamako me kyau a samo man Aloe Vera wanda ba hadi a rika shafawa gashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *