Ana amfani da Zuma ta hanyoyi da yawa dan magance matsalar fuska. A wannan rubutu, zamu kawo hanyoyi daban-daban na amfanin Zuma ga fuska.
Amfani da Zuma dan saka hasken fata:
Ana shafa zuma a fuska dan karawa fuska haske? Zumar ana iya hada ta da ruwa dan rage mata danko.
Ana shafawa a fuska na tsawon mintuna 15 zuwa 20 sannan a wanke.
Idan kwai tabon ciwo a fuska? Ana iya shafa zuma akan ciwon a barta ta dan dauki lokaci daga baya a wanke.
Hakan nasa tabon ciwon ya bace daga fuskar mutum. A yi sau da yawa dan samun sakamako me kyau.
Zuma tana kuma wanke dattin fuska tasa ainahin kalar fatar mutum ta bayyana ta hanyar cire matacciyar fatar data like a fuska.
[…] Hakanan ana amfani da Zuma wajan cire tabo a fuska, yanda ake yi shine, ana samun zuma me kyau a shafata a fuska, a bari ta yi mintuna 10 zuwa 15 sannan a wanke. Mun yi cikakken bayani kan yanda ake amfani da zuma wajan gyaran fuska. […]