
Shugaban kamfanin man Fetur na kasa, NNPCL, Bayo Ojulari ya bayyana cewa, Gyaran matatun man fetur din Najeriya ya zama alakakai.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi inda yace suna duba yiyuwar sayar da matatun man fetur din.
Yace an kashe makudan kudade wajan gyaran matatun man wanda an dade ana yi duk da sun samu ci gaba amma an fuskanci kalubale.