
Tauraron fina-finan Hausa, Kuma Mawaki, Garzali Miko yayi martani kan ganinshi da aka yi yana Loma a wajan Bikin Rarara da A’ishatulhumaira.
Hutudole ya kawo muku cewa, yanayin cin abincin da Garzali miko yayi da hannu yana loma a wajan ya jawo cece-kuce a wajan.
Saidai a wani sabon bidiyon an ga Garzali Miko yana cewa, shi haka ya saba cin abinci da hannu.
Yace ko a gobe ya samu dama da hannu zai ci abinci.