Monday, December 16
Shadow

Hanyoyin gyaran gashi

Kina son samun gashi me sheki, tsawo da lafiya?

Ga hanyoyin da zaki kula dashi yanda ya kamata kamar yanda likitoci masu kula da gashi suka tabbatar.

Ki kula da kalar gashinki sannan ki rika sayen man gashi wanda ya dace da kalar gashin kanki, watakila gashinki murdaddene, ko wanda yake a mike ne ko me kauri ne ko sirara ne, dan haka ki kula a wajan sayar da man gashi,mafi yawanci ana bayyana kalar gashin da ya kamata a yi amfani da kowane man gashi sai ki sayi wanda ya dace da gashin kanki.

A rika kula da gashi yayi maski ko ya yi datti a rika wankeshi: Ya danganta da kalar gashin kanki, misali idan gashin kanki me tsawo ne kuma matsirar gashin na fitar da maski sosai to ya kamata kina wankeshi duk wata.

Karanta Wannan  Gyaran gashi da wiwi

Idan kuma gashinki yawanci a bushe yake, yana da kauri, kuma murdaddene, to sai ki rika kula kina wankeshi duk sanda ya kamata kada dai ya wuce sati biyu zuwa uku ba’a wanke ba.

Idan kika ga gashinki na zuba, to mafi yawanci abinda ke kawoshi rashin wankeshine yanda ya kamata ko rashin amfani da man gashi da ya dace da gashinki.

A yayin da kike wanke gashin kanki da shampoo, ki rika saka yatsunki ciki sosai kina shafa man a matsirar gashin ki dan kawar da duk wani datti, saidai ki kiyaye busar da gashin kanki sosai.

A rika amfani da Conditioner bayan wanke gashi: Conditioner yana taimakawa sosai wajan gyara gashi.

Karanta Wannan  Gyaran Gashi

Ki bi a hankali wajan wanke gashin kanki, a yayin da gashin kai yake a jike, yana da saurin karyewa, dan haka a yi amfani da comb me tsinkaye masu wara-wara wanda akwai tazara sosai a tsakaninsu maimakon amfani da brush.

Sannan ki fara yiwa karshen gashin kanki Comb kamin ki shiga ciki sosai.

Idan Gashinki mikakke ne ki bari ya fara bushewa kamin ki sharceshi, idan kuma me lankwasane, da kauri, kina iya sharceshi ma a yayin da kike wanka.

A yayin da kike son busar da gashin kanki, kada ki saka tsumma ko tawul ki rika mummurzashi, hakan zai sa ya lalace, maimakon haka, ki sa tawul ko riga me kyau ki nadeshi a ciki har ruwan ya tsotse a hankali.

Karanta Wannan  Amfanin albasa a gashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *